Wani tsohon Kwamishina na hankoron Kujerar Tambuwal a jihar Sakkwato

Wani tsohon Kwamishina na hankoron Kujerar Tambuwal a jihar Sakkwato

Wani tsohon kwamishinan kudi na jihar Sakkwato, Farouk Malami Yabo, ya bayyana kudirin sa na neman takarar kujerar gwamnatin jihar karkashin inuwa ta jam'iyyar APC.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, Yabo ya sha alwashin fafatawa tare da gumurzu wajen kalubalantar gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal.

Yabo wanda ya rike mukamin kwamishina karkashin tsohuwar gwamnatin jihar ta Gwamna Aliyu Wamakko, ya sha alwashin kawo sauyin juya hali musamman a bangarori na habaka tattalin arziki tare da tallafawa matasa da mata wajen dogaro da kai.

Wani tsohon Kwamishina na hankoron Kujerar Tambuwal a jihar Sakkwato

Wani tsohon Kwamishina na hankoron Kujerar Tambuwal a jihar Sakkwato

Yake cewa, jihar Sakkwato na matukar bukatar wani sauyin yanayi musamman inganta tattalin arziki ta hanyar samar da ayyukan yi gami da kafa cibiyoyi na kasuwanci.

KARANTA KUMA: Sanata Soji Akanbi na nan a jam'iyyar sa ta APC - Majalisar Dattawa

Wannan babbar manufa za ta tabbatu ta hanyar bayar da muhimmiyar kulawa kan harkokin noma domin fitar da jihar daga wannan yanayi da take ciki a halin yanzu kamar yadda tsohon kwamishinan ya bayyana.

Kazalika Yabo ya nemi jam'iyyar su ta APC akan tabbatar da nasarar ta a babban zaben na kasa mai gabatowa a shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel