Gwamnatin Tarayya ta karkatar da wasu Biliyoyin kudi a 2016

Gwamnatin Tarayya ta karkatar da wasu Biliyoyin kudi a 2016

- Gwamnatin Tarayya ta kashe wasu kudi ba inda aka ware su ba a 2016

- Wani sabon bincike da Odita Janar yayi ne ya nuna wannan kwanan nan

Labari ya iso gare mu daga Jaridar nan ta The Cable cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta karkatar da wasu makudan kudi da su ka haura Naira Biliyan 28 shekaru 2 da su ka wuce.

Gwamnatin Tarayya ta karkatar da wasu Biliyoyin kudi a 2016

An wawuri wasu kudi wajen aikin da bai dace ba bayan hawan Gwamnatin APC

Mai bin diddikin yadda aka kashe kudin Gwamnatin Kasar ya fitar da wani rahoto inda ya nuna cewa akwai wasu kudin da aka ware domin maganin matsalolin kawararowar hamada da zaizayar kasa a wasu Jihohin Kasar nan.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari tayi sanadiyyar samawa mutane aikin yi ta harkar man fetur

Anthony Ayine wanda shi ne Odita Janar na kasar ya tabbatar da cewa an wawure kaso mafi tsoka daga cikin kudin da aka ware domin magance wadannan matsalolin. Oditan yace an kashe Biliyan 28 ne a wajen wasu ayyukan dabam.

Kashi 58% na wannan kudi da Gwamnatin Tarayya ta ware sun tafi ne wajen ayyukan da ba su da alaka da magance kwararowar hamada da cin kasa. Naira 28,239,060,570.89 Gwamnatin ta karkatar zuwa wasu harkokin gaban ta.

Babban Odita Janar na Kasar Anthony Ayine yayi kira ga Gwamnatin Kasar ta daina karkatar da kudin da aka kasafta da sunan wannan aiki zuw wani aikin na dabam. Akwai dai wasu bashi da Gwamnatin ta ci da ba a san ranar biya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel