Dalilin da yasa na shiga fadar shugaban kasa sau 3 a rana daya – Babban sufetan Yansanda

Dalilin da yasa na shiga fadar shugaban kasa sau 3 a rana daya – Babban sufetan Yansanda

Babban sufetan Yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris Kpotun ya musanta rahotannin dake yawo na cewa wai shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tsigeshi daga mukaminsa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kasa ya gayyaci IG ne sakamakon farmakin da jami’an Yansanda suka kai gidajen shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, da mataimakinsa Sanata Ike Ekweremadu a ranar Talata, 24 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya jaddada ba sulhu a tsakaninsa da duk makiyan jihar Kaduna

Dalilin da yasa na shiga fadar shugaban kasa sau 3 a rana daya – Babban sufetan Yansanda

Buhari da Babban sufetan Yansanda

Sai dai mashawarcin IG akan harkokin watsa labaru, Bala Ibrahim ya bayyana cewa babu inda shugaban kasa ya gayyaci IG zuwa fadar shugaban kasa a ranar Talata, amma IG ya tafi fadar shugaban kasa ne don radin kansa don ya gana da shugaba Buhari da mataimakinsa.

“Babu wanda ya gayyaci IG, amma don radin kansa yaje a dalilin tattaunawa da shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo, a wasu lokutta ma IG ya kan shiga Villa sama da sau uku.

“Ka san mataimakin shugaban kasa Farfesa ne a fannin Doka, don haka ne IG yake tuntubarsa don kauce ma yi ma doka karan tsaye.” Inji Bala.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel