Abin nema ya samu: Fayoshe ya kai ma Saraki ziyarar ‘Ana tare’

Abin nema ya samu: Fayoshe ya kai ma Saraki ziyarar ‘Ana tare’

Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Ayodele Fayoshe ya bayyana ma gwamnatin marasa Imani, biyo bayan farmakin da jami’an Yansanda suka kai ma shugaban majalisar dattawan Najeriya da mataimakinsa a gidajensu dake Abuja.

Fayose ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da ya kai gidan Saraki da Ekweremadu don nuna ana tare a ranar Talata, 24 ga watan Yuli, inda ya bayyana ziyarar tasa da nufin kara ma Sanatocin biyu kwarin gwiwa sakamakon tsangwamar da suke fuskanta daga hannun Yansanda.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya jaddada ba sulhu a tsakaninsa da duk makiyan jihar Kaduna

Abin nema ya samu: Fayoshe ya kai ma Saraki ziyarar ‘Ana tare’

Fayose da Saraki

“Haka zalika dalilin zuwana nan shine don na jinjina musu sakamakon namijin kokarin da suka yi wajen tsayawa tsayin daka tare da jajircewa a gudanar da aikinsu duk kuwa da barazanar da suke fuskanta daga gwamnatin marasa Imani.

“Gwamnatin marasa Imani tazo ne domin ta wargaza Najeriya, don haka ina fadi da babbar murya matsayata game da farmakin da Yansanda suka kai ma Sanatocin biyu, wannan abin Allah wadai ne, don haka nake kira ga Sanatocin da su cigaba da gwagwarmayar kwato Najeriya daga hannun yan mulkin kama karya.” Inji shi.

Daga karshe majiyar Legit.ng ta ruwaito Fayoshe ya jinjina ma Sanatoci goma sha biyar da suka sauya sheka daga APC, inda yace ya sun dade suna tsumayin ficewar Sanatocin daga APC zuwa PDP, inda yace ya zama wajibi a hada karfi da karfe don fatattakar gwamnatin Buhari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel