Sanatocin da ba su goyon bayan Saraki sun nemi su yi juyin mulki a Majalisa

Sanatocin da ba su goyon bayan Saraki sun nemi su yi juyin mulki a Majalisa

- An yi shirin karbe kujerar Bukola Saraki a Majalisar Dattawa

- Shugaban Majalisar yana jin haka kuwa ya zillewa ‘Yan Sanda

- Wasu manyan ‘Yan Majalisan APC ne su ka shirya wannan aiki

Mun samu labari cewa wasu Sanatocin da ba su goyon bayan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki sun nemi su tsige sa daga kujerar sa a jiya. Sai da ba su kai ga labari ba Bukola Saraki ya farga.

Sanatocin da ba su goyon bayan Saraki sun nemi su yi juyin mulki a Majalisa

'Yan Majalisan da ba su tare da Saraki sun yi yunkurin tsige sa jiya

Rahotanni daga Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa an yi yunkurin tsige Bukola Saraki da Mataimakin sa Ike Ekweremadu a Majalisar Dattawa. An shirya wannan ne bayan da aka sa Jami’an tsaro su ka zagaye gidan Saraki.

Mun samu labari cewa Bukola Saraki ya sulale ne daga gidan na sa inda ya tsere ya taho Majalisa. ‘Yan Sanda sun yi niyyan garkame sa domin su hana wasu ‘Yan Majalisar barin APC sai kuma ayi wuf a zabi wani sabon Shugaban a Majalisa.

KU KARANTA:

Wasu ‘Yan Majalisar da ke tare da Shugaban kasa sun yi niyyar amfani da wata doka a Majalisa na kafa shugabanni. Hakan zai sa a tsige Bukola Saraki da Mataimakin sa. Ana zargin su Sanata Ahmad Lawal ne da wannan danyen aiki.

Ana kuma zargin Ahmad Lawan da Ali Ndume su ka shirya wannan aiki ba tare da sanin wasu manyan Sanatocin APC irin su Sanata Abdullahi Adamu ba. Premium Times ta tuntubi Ali Ndume wanda ya nuna sam bai san maganar ba.

Wannan shiri dai bai ci tura ba inda Saraki ya zillewa ‘Yan Sanda yayi maza ya hau kan kujerar sa. Fitaccen Gwamnan PDP na Ekiti Ayo Fayose ya jinjinawa tsofaffin ‘Yan Majalisun APC da su ka sauya sheka su ka dawo PDP a jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel