Boko Haram ta saki sabuwar bidiyo, Shekau ya yi kira ga hallaka kafirai (Kalli bidiyon)

Boko Haram ta saki sabuwar bidiyo, Shekau ya yi kira ga hallaka kafirai (Kalli bidiyon)

Shugaban kungiyar yan tada kayar bayan Boko Haram ya yi kira ga mayakansa su rike aqidan Islam idan suna son samun nasara kan kafirai.

A wata sabuwar bidiyon da dan jarida Ahmed Salkida ya samu kuma ya mikawa jaridar Sahara Reporters, Shekau ya yi kira ga mayakansa su hallaka kafirai, su harbesu a duk hanyar da suka ga dama domin tsarkake kasa.

Bidiyon ya nuna Shekau sanye da fararen kaya kuma bindiga AK47 a daga cikin wuraren da suke boye

Bidiyon ya fara da nuna yadda ake horar da matasan kungiyar yadda zasu yaki jami’an tsaron Najeriya.

Kalli bidiyon:

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel