Sanata Soji Akanbi na nan a jam'iyyar sa ta APC - Majalisar Dattawa

Sanata Soji Akanbi na nan a jam'iyyar sa ta APC - Majalisar Dattawa

A ranar Talatar da gabata ne jam'iyyar APC ta rasa kimanin 'yan Majalaisar tarayya 50 yayin da suka sauya sheka daga jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyun adawa musamman jam'iyyar PDP.

Cikin jerin Sanatoci da suka fice daga jam'iyyar ta APC zuwa PDP da majalisar dattawa ta lissafo ta hadar har da Sanata Rilwan Adesoji Akanbi kamar yadda ta bayyanawa mabiyan ta cikin shafin ta na dandalin sada zumunta na twitter.

Sai dai Majalisar tayi wannan amai kuma ta lashe abin ta yayin da ta yi karin hakse dangane da wannan jita-jita da ta yadawa al'ummar kasar nan da cewar Sanata Akanbi ya koma karkashin inuwa ta lemar jam'iyyar PDP.

Sanata Soji Akanbi na nan a jam'iyyar sa ta APC - Majalisar Dattawa

Sanata Soji Akanbi na nan a jam'iyyar sa ta APC - Majalisar Dattawa

Majalisar kamar yadda shafin jaridar nan ta The Punch ya ruwaito ta bayyana cewa, Sanatan na nan daram cikin jam'iyyar sa ta APC domin kuwa bai bi sahun wadanda suka yi hannun riga da ita ba.

KARANTA KUMA: Ka rika kiyaye lafuzan ka - Ngige ya gargadi Oshiomhole

Legit.ng ta fahimci cewa, Sanata Soji Akanbi shine dattijon dake wakilcin mazabar Kudancin jihar Oyo a majalisar ta dattawa.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Ministan Kwadago, Sanata Chris Ngige ya gargadi shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole kan yiwa harshen sa linzami wajen furta zantuttukan da ba ya da tabbacin a kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel