Ku kyale Hukumomin tsaro su gudanar da ayyukan su - Fadar Shugaban Kasa

Ku kyale Hukumomin tsaro su gudanar da ayyukan su - Fadar Shugaban Kasa

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, fadar shugaban kasa ta yi la'akarin cewa ana yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari izgili da cin fuskar sa a duk sa'ilin da aikin hukumomin tsaro na kasar nan ya biyo ta kan manya ko mashahuran mutane domin gudanar da bincike ko zartar da hukunci.

A ranar Talatar da ta gabata ne fadar shugaban kasar ta bayyana hakan da cewa, ana yawaita sukar jagoran kasar nan tare da furta kalamai na tsageranci a kansa yayin da hukumomin tsaro na kasar nan ke yunkurin sauke nauyin da rataya a wuyan su kan wasu manyan mutane a kasar nan.

Cikin sanarwar da babban hadimi akan hulda da manema labarai ga shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ya gabatar ya bayyana cewa, duk wata doka ta kasar nan tana kan kowa, kazalika ba a iyakance ta kan talakawa ko mafi ƙasƙanci a cikin ta ba.

Ku kyale Hukumomin tsaro su gudanar da ayyukan su - Fadar Shugaban Kasa

Ku kyale Hukumomin tsaro su gudanar da ayyukan su - Fadar Shugaban Kasa

Yake cewa, "akwai ban mamaki, takaici tare da rashin aikata daidai dangane da yadda gama garin mutane za su amsa kiran duk wata hukuma yayin da bincike ya biyo ta kansu amma mashahuran mutane ke nuna fifiko tare da tsageranci yayin da dokar ta biyo ta kansu."

"Ba bu ta yadda za a yi kasar nan ta cimma wani ci gaba ta fuskar zaman lafiya muddin ya kasance ana sanya siyasa zartar da dokoki tare da hukuncin da iyakance wadanda doka za ta hau kawunan su a kasar nan."

Mallam Garba ya ci gaba da cewa, hukumomin tsaro na gudanar da ayyukan su ne bisa tanadi na kundin tsari da dokokin kasa suka shar'anta. "Saboda haka 'yan Naeriya su fahimci cewa wannan gwamnatin shugaba Buhari ce mai daukar al'ummarta a matsayin bai daya ta fuskar zartar da duk wani hukunci ko doka."

KARANTA KUMA: Sauya shekar Kwankwaso zuwa PDP alheri ne ga Ganduje - Iliyasu Kwankwaso

"Kazalika kundin tsari ya yiwa hukumomin tsaro tanadi da shar'anta nauyin gudanar da bincike kan duk wani zargi na sabawa dokokin kasar nan ba tare da iyakance duk wasu masu hannu cikin laifin ba."

"Shugaba Buhari ba ya da iko ko wani hurumi na yiwa duk wata hukumar tsaro katsalandan cikin sauke nauyin da kundin tsari ya gindaya a kanta. Babban aminin doka na hakika shine wanda ya kiyaye ta."

Cikin sanarwar Mallam Garba ya kara da cewa, "duk wanda ake zargin sa da laifi yana da dama da gabatar da kansa gaban domin tabbatar da gaskiyar sa a madadin fita ɓaɓatun neman afuwa ko yafiya a hannun al'umma."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel