Gwamnan Jihar Kogi ya jefa al’umma cikin matsala da 'dan-karen bashi

Gwamnan Jihar Kogi ya jefa al’umma cikin matsala da 'dan-karen bashi

Duk da irin kokarin da Gwamnatin Tarayya tayi na biyan Gwamnonin Jihohi bashi domin su biya Ma’aikata har yanzu Jihar Kogi ba ta cika wannan alkawari ba kamar yadda mu ka samu labari.

Jaridar Premium Times ta kasar nan ta rahoto cewa har yanzu Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya kan karbi bashi ne daga hannun bankuna domin ya biya albashin Ma’aikata da sauran hakkokin Jama’an Jihar Kogi a kowane wata.

Gwamnan Jihar Kogi ya jefa al’umma cikin matsala da 'dan-karen bashi

Ana bin Jihar Kogi bashin sama da Naira Biliyan 100

Tun farkon 2018 ne Gwamna Yahaya Bello da yake APC ya fara cin bashi daga bankunan kasuwa yana biyan albashin Ma’aikata. Daga Watan Junairu zuwa yanzu Gwamnan na Kogi ya karbi bashin abin da ya haura Naira Biliyan 30.

KU KARANTA: An fara bibiyar Ganduje ko zai jefar da jar hula bayan Kwankwaso ya koma PDP

Abin mamakin dai shi ne yadda aka rasa inda Gwamnan ya kai kudin da Gwamnatin Tarayya ta aiko masa da shi domin ya biya albashi. Shugaba Buhari dai ya turawa Jihar Kogi Naira Biliyan 50 amma har yanzu Jihar na cin bashi.

Yanzu haka dai ana sa Kogi a cikin Jihohin da bashi yayi mata katutu. Jihar Kogi na da bashin da ya haura Naira Biliyan 100 yanzu a kan ta. A karshen bara ne Gwamna Bello ya biya Ma’aikata albashin su na kusan watanni 4 da su ka makale.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel