Gwamna El-Rufai ya jaddada ba sulhu a tsakaninsa da duk makiyan jihar Kaduna

Gwamna El-Rufai ya jaddada ba sulhu a tsakaninsa da duk makiyan jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa babu sulhu a tsakaninsa da duk wasu yan siyasa da ta tabbata makiyan al’ummar jihar Kaduna ne, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito El-Rufai ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawuna, Samuel Aruwan, inda yace yana sane da cewa shuwagabannin jam’iyyar APC na jihar Kaduna na yunkurin harhada kan yan siyasan jihar.

KU KARANTA: Wani Sanata daga cikin Sanatoci 15 da suka fice daga APC ya karyata ficewarsa

Gwamna El-Rufai ya jaddada ba sulhu a tsakaninsa da duk makiyan jihar Kaduna

Gwamna El-Rufai

Ya kara da cewa Gwamnan na goyon bayan wannan yunkuri, amma fa babu wanda zai sulhunta shi da yan siyasan da suka tabbatar da kansu a matsayin makiyan al’ummar jihar Kaduna.

“El-Rufai na sane da irin yunkurin da shugaban jam’iyyar APC Air Commodore EammnuelJekada ke yin a kokarin sulhunta sassan jam’iyyar APC da basa ga maciji a jihar, amma fa gwamna ba zai sulhunta da makiyan jihar Kaduna ba.” Inji shi.

Daga cikin wadanda gwamnan ke da tsatstsamar dangantaka dasu akwai Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi da Sanata Lar, sauran sun hada da tsohon shugaban jam’iyyar Hakim Baba Ahmed, Isa Ashiru da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel