Har yanzu APC ke da rinjaye a majalisar wakilai, duba shaida

Har yanzu APC ke da rinjaye a majalisar wakilai, duba shaida

Shugaban 'yan jam'iyyar APC na majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila daga jihar Legas ya shaida wa manema labarai cewa wadanda suka fice daga jam'iyyar ta APC suna neman tikitin zabe ne gabanin babban zaben shekarar 2019.

Gbajabiamila yace duk da ficewarsu, APC ce ke da rinjaye a majalisar inda take da mambobi 192, PDP na da mambobin 156, APGA na da 5, ADC na da 4, Accord Party 1, SDP 1 sai kuma akwai gibin kujera daya na dan majalisa da ya rasu.

'Yan majalisa 37 da suka fice daga jam'iyyar ta APC a yau Talata sun bayyana cewa 'cin zarafi da kuntatawa mambobin jam'iyyar masu mabanbantan ra'ayi da akeyi' yasa suka fice daga jam'iyyar.

Har yanzu APC ke da rinjaye a majalisar wakilai, duba shaida

Har yanzu APC ke da rinjaye a majalisar wakilai, duba shaida

KU KARANTA: Tsalle-Tsallen 'yan siyasa: Wani dan majalisar PDP ya fice daga jam'iyyar

Tawagar sanatocin da suka koma jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Razak Atunwa (PDP, Kwara) yace sun shiga APC a shekarar 2014 ne saboda sunyi imani cewa jam'iyyar zata kawo canji na cigaba amma a daga baya jam'iyyar ta fara nufar hanyar rugujewa a cewarsa.

Cikin mambonin da suka fice daga jam'iyyar ta APC 37, wasu daga ciki sun shiga jam'iyyar PDP, wasu kuma sun koma jam'iyar African Democratic Party, ADC.

Wasu daga cikin wanda suka koma PDP sun hada da Ahmed Chachangi (Kaduna), Razak Atunwa (Kwara), Aliyu Madaki (Kano), Hassan Saleh (Benue), Mark Gbillah (Benue), Aliyu Pategi (Kwara), Aminu Shagari (Sokoto), Abdulsamad Dasuki (Sokoto), Emmanuel Oker-Jev (Benue), Nasir Garo (Kano).

Saura sune Zacharia Mohammed (Kwara), Hassan Omale (Benue), Funke Adedoyin (Kwara), Tope Olayuonu (Kwara), Dickson Takir (Benue), Bode Ayorinde (Ondo), Ali Madaki (Kano).

'Yan majalisa hudu da suka koma ADC sune: Taiwo Akintola (Oyo), Olufemi Samson (Oyo), Sunday Adepoju (Oyo) da Wole Olasupo (Oyo).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel