Shugaba Buhari yaki amincewa da wasu dokoki 5 da majalisa ta yi

Shugaba Buhari yaki amincewa da wasu dokoki 5 da majalisa ta yi

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa ya sanya hannu kan wasu sabbin dokoki biyar na bukatar yin gyara a kundin tsarin mulkin kasa da majalisar wakilai ta tarayya ta nemi sahalewarsa a kai kamar yadda Today Ng ta wallafa.

Buhari ya sanar da majalisar ne cikin wata rubutacciyar wasika da ya aikawa Majalisar ta wakilai inda Kakakin majalisar, Yakubu Dogara, ya gabatar yayin zaman majalisar da aka gudanar a ranar yau ta Talata.

Shugaban majalisar, ya lissafa dokokin da da majalisar take bukatar yiwa kwaskwarima wanda suka hada da kudiri mai lamba takwas, 15, 22, 24 da kuma 28.

Shugaba Buhari yaki amincewa da wasu dokoki 5 da majalisa ta yi

Shugaba Buhari yaki amincewa da wasu dokoki 5 da majalisa ta yi

DUBA WANNAN: Tsalle-Tsallen 'yan siyasa: Wani dan majalisar PDP ya fice daga jam'iyyar

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaban kasar ya sanar da majalisar cewa ya ki amincewa da kudiri mai lamba takwas ne saboda akwai gyaran da ya dace majalisar tayi, ya kuma bayyana cewa dokar maimaici ne saboda akwai wasu sassan kundin tsarin mulki da su kayi kamanceceniya da ita.

A kan doka mai lamba 22, shugaba Buhari yace wasu daga cikin ayyukan da majalisar ta lissafa ayyukan a matsayin ayyukan hukumar farin hula na NSCDC, ayyuka ne da wasu cibiyoyin gwamnati ke gudnarwa.

Sauran dokokin ma, shugaban kasar ya bayyana matsalolin da yasa bai amince dasu ba a cikin wasikar da ya aike wa majalisar.

Idan mai karatu bai manta ba, shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da wasu dokoki hudu da majalisar tarayyar ta aike masa cikin makonnin da suka wuce.

Cikin kwanakin nan ne majalisar wakilai ta saka gabatar da wasu dokoki 11 da Shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa dasu da nufin yin amfani da karfin doka don su zartar dasu ba tare da amincewarsa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel