Mutane 4 sun shiga hannu da laifin yiwa kamfanin MTN ɓarna

Mutane 4 sun shiga hannu da laifin yiwa kamfanin MTN ɓarna

Kamar yadda shfin jaridar The Nation ya ruwaito mun samu rahoton cewa, kimanin mutane hudu ne suka shiga hannun hukuma bisa laifin yiwa kamfanin nan na sadarwa na MTN ɓarna a yankin Mowo na unguwar Badagry a jihar Legas.

Wannan mutane masu tayar da zaune tsaye sun hadar da, Monday Ogbonna, Bamiji Akanni, Sunday Odewale da kuma Anthony Ivie da sun aikata ta'asar ne a ranar 17 ga watan Yuli kamar yadda rahotanni suka zayyana.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan maɓarnata sun yi amfani da wata Mota kirar Mazda mai lambar MUS 175 XW wajen yashe kayan aiki masu tabbatar da ingancin sadarwa na kamfanin MTN dake yankin Mowo.

Mutane 4 sun shiga hannu da laifin yiwa kamfanin MTN ɓarna

Mutane 4 sun shiga hannu da laifin yiwa kamfanin MTN ɓarna

An cafke wannan mutane masu son banza a unguwar Oshodi ta jihar Legas kamar yadda kwamishinan 'yan sanda Imohimi Edgal ya bayyana.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya Jami'an tsaro suka yiwa Gidan Saraki kawanya

Edgal ya bayyana cewa, wannan miyagun mutane sun yi awon gaba ne da wasu muhimman kayan aiki na sadarwar zamani masu tabbatar da ingancin ta masu ga masu amfani da wayoyin salula da sauran kayayyaki masu amfani da fasahar zamani makamacin ta.

Ya kara da cewa, a halin yanzu dai an ci gaba da gudanar da bincike inda za a gurfanar dasu gaban kuliya domin zartar masu da hukuncin da ya dace da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel