Na sauya sheka ne zuwa ADC ba PDP ba - Sanata

Na sauya sheka ne zuwa ADC ba PDP ba - Sanata

Sanata mai wakiltan mazabar Oyo ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Monsurat Sunmonu, tayi bayanin dalilinta na sauya sheka daga jm’iyyar APC mai mulki.

Sanatan ta bayyana cewa ta sauya sheka ne zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba wai jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba.

Misis Sunmonu tare da sanatoci 14 ne suka sauya sheka daga APC, a safiyar ranar Talata, 24 ga watan Yuli.

Da yake sanar da sauya shekarsu a wata wasika sa hannun sanatocin, Sarak ya ce sanatocin sun koma PDP.

Na sauya sheka ne zuwa ADC ba PDP ba - Sanata

Na sauya sheka ne zuwa ADC ba PDP ba - Sanata

Tsawon watanni da dama kenan da Misis Sunmonu da wasu yan APC a Oyo suka samu sabani da gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

KU KARANTA KUMA: Yadda na zille wa jami’an tsaro – Bukola Saraki

Ta bayyana cewa ta sauya sheka ne saboda rikicin jam’iyyar da aka kasa sasantawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel