Komawar Kwankwaso PDP babbar nasara ce ga Ganduje wurin lashe zaben 2019

Komawar Kwankwaso PDP babbar nasara ce ga Ganduje wurin lashe zaben 2019

Shugaban majalisar gwamnatin jihar Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata yace canja shekar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba wani abun mamaki bane, ganin daman inda Sanatan ya nuna son zuciyar shi a fili

Komawar Kwankwaso PDP babbar nasara ce ga Ganduje wurin lashe zaben 2019

Komawar Kwankwaso PDP babbar nasara ce ga Ganduje wurin lashe zaben 2019

Shugaban majalisar gwamnatin jihar Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata yace canja shekar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba wani abun mamaki bane, ganin daman inda Sanatan ya nuna son zuciyar shi a fili.

DUBA WANNAN: Ko a jikin mu canja shekar da kuke yi - Jam'iyyar APC

Da yake magana da manema labarai, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata ya tabbatar da cewar canja shekar tashi ba zai shafi jam'iyyar APC ba, sannan kuma ba zai hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje maye kujerar shi ba a karo na biyu a zabe mai gabatowa na shekarar 2019.

A jiya ne dai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da wasu Sanatoci na kasar nan suka canja sheka daga babbar jam'iyya mai mulki ta APC zuwa babbar jam'iyyar adawa wato PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel