Da duminsa: An tsige shugaban majalisa 'dan APC a jihar arewa da gwamna ke shirin canja sheka

Da duminsa: An tsige shugaban majalisa 'dan APC a jihar arewa da gwamna ke shirin canja sheka

Majalisar jihar Benue ta tsige Honourable Terkimbi Ikyange na jam'iyyar APC a matsayinsa na kakakin majalisar kamar yadda Channels tv ta wallafa.

Majalisar ta tsige Ikyange ne bayan wani dan majalisa mai suna Richard Ujege mai wakiltan yankin Konshisa a ya gabatar kudirin gazawa a kan Ikyange a gaban majalisar.

Kudirin ta samu goyon bayan 'yan majalisar 21 cikin 30 dake majalisar.

Da duminsa: An tsige shugaban majalisa 'dan APC a jihar arewa da gwamna ke shirin canja sheka

Da duminsa: An tsige shugaban majalisa 'dan APC a jihar arewa da gwamna ke shirin canja sheka

An tsige kakakin majalisar ne duk da cewa bai hallarci zaman da akayi ba amma akawun majalisar ya hallarci zaman tsige kakakin majalisar.

DUBA WANNAN: R-APC zata iya tsayar da dan takarar shugaban kasa - Buba Galadima

Wannan tsigewar tasa tana zuwa ne bayan wasu 'yan masa sama da 32 sun fice daga jam'iyyar APC a majalisar wakilai ta tarayya.

Kazalika, wasu Sanatoci a majalisar Dattawa suma sun bayyana ficewarsu daga jam'iyyar ta APC a wata wasilka da Shuagaban majalisa Bukola Saraki ya karanta a yau kuma daga baya majalisar ta dage zamanta har zuwa watan Satumba.

An dai jima an samun korafe-korafen daga wasu mambobin jam'iyyar ta APC musamman wanda suka ware kansu suka kafa sabuwar APC ko kuma r-APC. Ficewar nasu bai bawa mutane mamaki ba tunda sun dade suna barazana cewa zasu fice din.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel