2019: Har yanzu mu muke da mafi rinjaye - Jam'iyyar APC

2019: Har yanzu mu muke da mafi rinjaye - Jam'iyyar APC

Babbar jam'iyya mai mulki wato All Progressives Congress (APC) ya tabbatar wa da mambobin ta cewar har yanzu itace take da rinjaye a zaben shekara mai gabatowa na 2019

2019: Har yanzu mu muke da mafi rinjaye - Jam'iyyar APC

2019: Har yanzu mu muke da mafi rinjaye - Jam'iyyar APC

Babbar jam'iyya mai mulki wato All Progressives Congress (APC) ya tabbatar wa da mambobin ta cewar har yanzu itace take da rinjaye a zaben shekara mai gabatowa na 2019, duk kuwa da irin sauya shekar da mahukuntan kasar keyi suna koma babbar jam'iyyar adawa wato PDP.

DUBA WANNAN: Fashin Offa: Hukumar 'Yan Sanda sun nemi Saraki sama da kasa sun rasa

Sakataren yada labarai na jam'iyyar APC, Malam Bolaji Abdullahi, shine ya tabbatar da hakan jiya a wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar wacce ke da alaka da komawar Sanatoci 16 da 'yan majalisar tarayya 37 suka yi zuwa jam'iyyar PDP.

Jam'iyyar ta tabbatarwa da al'umma cewar har yanzu itace take da mafi rinjayen jihohi, inda take da jihohi 25 a cikin 36, sannan kuma itace take da mafi rinjaye a majalisar tarayya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel