Yadda na zille wa jami’an tsaro – Bukola Saraki

Yadda na zille wa jami’an tsaro – Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya bayyana yadda ya zille wa jami’an ‘yan sandan da suka kewaye gidan sa da nufin hana shi fita zuwa majalisa a safiyar yau, Talata 24 ga watan Yuli.

Ya ce duk da mamaye gidan sa da yan sandan suka yi, hakan bai hana shi isa zauren majalisa da misalin karfe 10:40 na safe ba.

A cewar Saraki, “Ni dama tuni tun jiya na kwana da shirin cewa hakan na iya faruwa. Domin haka da shiri na na kwana.

“Mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya kira ni kan cewa ba zai iya zuwa ba, saboda shi ma jami’an tsaro sun mamaye gidan sa.

“Tun karfe 6:30 aka tare titin gida na, ba shige kuma ba fice.

“An jera motoci na tun safe, amma aka hana kowane direba motsawa daga inda ya ke tsaye da mota.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya gana da Buhari, yayi Magana kan sauya shekar yan majalisa daga APC

A karshe dai ya ce Allah ne ya kubutar da shi har ya kai kan sa majalisa, inda ya na zuwa ya shiga zauren zaman majalisa.

A halin da ake ciki, babban hadimi na musamman ga shugaban majalisar akan harkokin hulda da manema labarai, Mista Yusuph Olaniyonu ya bayyana cewa, jami'an tsaron sun aiwatar da hakan ne domin hana wasu Sanatoci sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Olaniyonu dai ya bayyana cewa, babbar manufar hana Saraki ficewa daga gidan sa ita ce dakile zaman majalisar da yake jagoranta domin katse shirin sauyin sheka na wasu daga cikin jiga-jigan majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel