Sai an ɗauki tsawon shekaru 22 na gyaran ɓarnar Aregbesola - Omisore

Sai an ɗauki tsawon shekaru 22 na gyaran ɓarnar Aregbesola - Omisore

Wani tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore ya bayyana cewa, sai an dauki tsawon shekaru 22 na gyaran ɓarnar gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Rauf Aregbsesola.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Omisore ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a babban birnin kasar nan na Abuja bayan amsar takardar shaidar dawowar sa jam'iyyar SDP.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta bayyana, tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne sakamakon kantar bashi da gwamnatin jihar ke fama da ita.

Sai an ɗauki tsawon shekaru 22 na gyaran ɓarnar Aregbesola - Omisore

Sai an ɗauki tsawon shekaru 22 na gyaran ɓarnar Aregbesola - Omisore

Omisore wanda ke neman takarar gwamna a jihar karkashin jam'iyyar ta SDP ya bayyana cewa, ana amfani fiye da rabi na kasafin jihar daga asusun gwamnatin tarayya wajen kokarin sauke nauyin bashin da gwamnatin Aregbesola ta jefa su ciki a halin yanzu.

Yake cewa, wannan shine musabbabin da ya sanya gwamnatin jihar ke gazawa wajen biyan albashin ma'aikata, tare da rashin kawo wani muhimmin ci gaba cikin jihar musamman ta fuskar gine-gine da kiwon lafiya.

KARANTA KUMA: Yadda Tsohon Sufeto Janar, Marigayi Ibrahim Coomassie ya bayar da umarnin damuka da garkame ni gidan kaso na Kirikiri - Shehu Sani

A yayin tuntubar sa dangane da yadda ai bunkasa samar da kudaden shiga a jihar, Omisore ya bayyana cewa zai bai wa harkar noma muhimmiyar kulawa domin tabbatar da hakan.

Kwamishinan yada labarai da bayanai na jihar, Mista Adelani yayin mayar da martani ya bayyana cewa, ya kamata Omisore ya rike mutuncin sa sakamakon wannan karairayi da shirga tare da wanke kansa a dangane da tuhumar da hukumar EFCC ta malala a gare sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel