Guguwar canjin sheka: APC zata maka ‘yan majalisar da suka fice a kotu

Guguwar canjin sheka: APC zata maka ‘yan majalisar da suka fice a kotu

Mambobin majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC sun yi watsi da batun canjin shekar da wasu daga cikinsu suka yi a yau, Talata.

Mambobin na APC, tab akin shugaban masu rinjaye a majalisar, Femi Gbajabiamila, sun sanar da cewar zasu dauki matakan shari’a a kan ‘yan mambobin da suka fice.

Kimanin mambobin majalisar ta wakilai 37 ne suka fita daga jam’iyyar APC mai mulki a yau, 33 sun canja sheka ne zuwa PDP yayin da wasu 4 daga jihar Osun suka koma sabuwar jam’iyyar ADC, ta tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Guguwar canjin sheka: APC zata maka ‘yan majalisar da suka fice a kotu

Majalisar wakilai

Da yake Magana a madadin ragowar mambobin jam’iyyar APC a majalisar wakilai, Gbajabiamila, ya bayyana cewar canjin shekar abokan aikin nasu ya saba ka’ida.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen 'yan majalisar wakilai da suka fice daga APC

“Babu rudani dangane da abinda suka aikata, sashe na 68 ya gama warware komai dangane da canjin shekar jam’iyyar dan majalisa. A saboda haka zamu bawa uwar jam’iyya karfin gwuiwar tafiya kotu domin daukan matakin day a dace a kan su,” a cewar Gbajabiamila.

Sannan ya cigaba da cewa, “Jama’a ne suka zabe su a karkashin tutar APC, kujerar mallakar jam’iyya ce, a saboda haka duk wanda ya bar jam’iyya ba zai tafi da abinda yake na jam’iyyar ba.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel