Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya gana da Buhari, yayi Magana kan sauya shekar yan majalisa daga APC

Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya gana da Buhari, yayi Magana kan sauya shekar yan majalisa daga APC

Shugaban jam’iyyar Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa yana farin ciki da cewar wasu mambobin majalisar dattawa da na wakilai sun bar jam’iyyarsa zuwa jam’iyyun adawa.

Mista Oshiomhole wadda yayi Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 24 ga watan Yuli yace wadanda suka sauya shekar sun kasance yan baranda wadanda dama sun zo APC ne don kawai su yi nasarar zabe.

Ya ce jam’iyya mai mulki bata damu ba ko kadan sannan kuma cewa baya hana kansa bacci saboda sauya shekar.

Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya gana da Buhari, yayi Magana kan sauya shekar yan majalisa daga APC

Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya gana da Buhari, yayi Magana kan sauya shekar yan majalisa daga APC

Oshiomhole ya kuma bayana cewa yana da kyau cewa wadanda basu taba yi imani da APC ba suna barinta gabannin zaben saboda hakan zai ba jam’iyyar damar maida hankali wajen yakin neman zabenta.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda na jiran isowar Saraki ofishin IRT a Abuja kan fashin Offa

Yace wadanda suka sauya sheka ba zasu iya hana APC nasara ba saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari na da kur’u fiye da nasu a mazabunsu a zaben da ya gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel