Da dumi dumi: Buhari ya yi ma babban Sufetan Yansanda gayyatar gaggawa

Da dumi dumi: Buhari ya yi ma babban Sufetan Yansanda gayyatar gaggawa

A yanzu haka babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris Kpotun yana fadar shugaban kasa tun safe biyo bayan wata gayyatar gaggawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa, amma har zuwa yanzu bai samu ganawa da Buharin ba, kuma ba a bashi umarnin komawa ofishinsa ba.

Daily Nigerian ta ruwaito wannan gayyata da Buhari ya yi ma IG baya rasa nasaba da farmakin da jami’an Yansanda suka kai zuwa gidan shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa Sanata Ike Ekweremadu da safiyar Talata, 24 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Kida ya canza, rawa ya canza: Shekewar Kwankwaso zuwa PDP ya sauya lissafin majalisar dattawa

Da dumi dumi: Buhari ya yi ma babban Sufetan Yansanda gayyatar gaggawa

Buhari da IG

“Shugaban kasa da mataimakinsa tare da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari sun shiga wata ganawar sirri game da IG, inda suka barshi a waje yana jiransu, da wannan akwai alamun Buhari zai tsige IG don kuwa mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Abba Kyari sun fara shirya takardar sallamarsa.” Inji wata majiya mai karfi.

Bugu da kari majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin wadanda ke sahun gaba wajen ganin an tsige IG akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole.

Sai dai duk kokarin da Yansanda suka yi na kama Saraki tare da hana shi zuwa majalisa bai yiwu ba, inda shi ma yayi nasa shirin irin na badda kama, kuma ya sulala majalisar ba tare da sun ankara da shi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel