Dalilin da ya sanya Jami'an tsaro suka yiwa Gidan Saraki kawanya

Dalilin da ya sanya Jami'an tsaro suka yiwa Gidan Saraki kawanya

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana mun samu rahoton cewa, da sanyin safiyar yau ta Talata ne wasu jami'an tsaro na 'yan sanda suka yi kawanya a gidan shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, tare da hana shige da fice.

Sai dai babban hadimi na musamman ga shugaban majalisar akan harkokin hulda da manema labarai, Mista Yusuph Olaniyonu ya bayyana cewa, jami'an tsaron sun aiwatar da hakan ne domin hana wasu Sanatoci sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Olaniyonu dai ya bayyana cewa, babbar manufar hana Saraki ficewa daga gidan sa ita ce dakile zaman majalisar da yake jagoranta domin katse shirin sauyin sheka na wasu daga cikin jiga-jigan majalisar.

Dalilin da ya sanya Jami'an tsaro suka yiwa Gidan Saraki kawanya

Dalilin da ya sanya Jami'an tsaro suka yiwa Gidan Saraki kawanya
Source: Depositphotos

Kamar yadda hadimin ya bayyana, haddasa wannan jinkiri na sauyin shekar kan iya sanya wasu sauya ra'ayin su kamar yadda hausawa kan ce a jira ya huce shike sanyawa a ci da rabon wani.

KARANTA KUMA: Dalilin Kyakkyawar alakar dake tsakanin Shugaba Buhari da Gwamna Umahi

Ya kara da cewa, mafi akasarin masu shirin sauyin shekar na iya sauya taku da salo domin gujewa barazanar da ka iya afka masu.

Kazalika Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan kawanya ta jami'an tsaro ba ta tsaya iya gidan shugaban majalisar ba domin kuwa ta hadar har da Mataimakin sa, Ike Ekweremadu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel