Zamanin sauyin sheka: Yan majalisar APC guda 37 sun sheke zuwa PDP

Zamanin sauyin sheka: Yan majalisar APC guda 37 sun sheke zuwa PDP

Wani rahoto da muka samu da dumi dumi yanzun nan ya tabbatar da cewa akalla yayan majalisar wakilan Najeriya su Talatin da bakwai ne suka yi fatali da jam’iyyar APC, suka rungumi jam’iyyar PDP.

Daga cikin wadanda suka fice daga APC, guda Talatin da biyu sun koma PDP, yayin da wasu guda hudu suka koma suka koma ADC, daga bisan aka samu wani guda daya da ya bayyana sanar da yin murabus daga APC, amma bai bayyana inda ya dosa ba.

KU KARANTA: Kida ya canza, rawa ya canza: Shekewar Kwankwaso zuwa PDP ya sauya lissafin majalisar dattawa

Zamanin sauyin sheka: Yan majalisar APC guda 37 sun sheke zuwa PDP

Majalisar wakilai

Sanannu daga cikin wadanda suka fice sun hada da Sani Rano, Barry Mpigi, Ali Madaki, Dickson Tackighir, Hassan Saleh, Danburam Nuhu, Mark Gbilah, Razak Antunwa, Ahmed Bichi, Abdulsamad Dasuki da Zakari Mohammed.

Sai dai Legit.ng ta ruwaito ba’a ambaci sunan Kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da na mataimakinsa Yusuf Lasun ba a cikin yan majalisun da suka yi hannun riga da APC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel