Ina cikin hatsari – Melaye ya nemi 'doki kan barazana ga rayuwarsa a zauren majalisa

Ina cikin hatsari – Melaye ya nemi 'doki kan barazana ga rayuwarsa a zauren majalisa

Sanata mai wakiltan Kogi na yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye ya nemi doki kan zargin kokarin kashe sa da ake shirin yi.

Legit.ng ta rahoto cewa Melaye a ranar Talata, 24 ga watan Yuli, yayinda yake nuni ga umurni 14 na hukuncin majalisar dattawa, yayi zargin cewa yan sanda sun yi yunkurin kashe shi yayinda yake barin mahaifarsa, Kogi.

Melaye na daga cikin sanatocin jam’iyyar APC goma sha biyar da suka sauya sheka zuwa PDP a majalisa a ranar Talata, 24 ga watan Yuli.

Ina cikin hatsari – Melaye ya nemi doki kan barazana da rayuwarsa a zauren majalisa

Ina cikin hatsari – Melaye ya nemi doki kan barazana da rayuwarsa a zauren majalisa

Da yake martani akan Melayi, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki yace ya ji dadin ganin sanatan Kogin, inda ya kara da cewa zai ci gaba da tabbatar da cewar sun kare kansu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP sun amince da bukatar R-APC, sun shirya canza suna

A baya mun rahoto cewa, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi martani akan sauya shekar sanatocin APC goma sha biyar zuwa jam’iyyarta a ranar Talata, 24 ga watan Yuli.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel