PDP ta yi sharhi akan sauya shekar sanatocin APC 15 zuwa jam’iyyar adawa, ta bayyana kanta a matsayin mafi rinjaye a majalisa

PDP ta yi sharhi akan sauya shekar sanatocin APC 15 zuwa jam’iyyar adawa, ta bayyana kanta a matsayin mafi rinjaye a majalisa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi martani akan sauya shekar sanatocin APC goma sha biyar zuwa jam’iyyarta a ranar Talata, 24 ga watan Yuli.

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a ranar Talata, 24 ga watan Yuli a zauren majalisa ya sanar da sauya shekar sanatoci daga jam’iyya mai mulki zuwa PDP.

A shafinsa na twitter, kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya bayyana sauya shekar a matsayin habbaka ga jam’iyyar domin nasara a zaben 2019.

PDP ta yi sharhi akan sauya shekar sanatocin APC 15 zuwa jam’iyyar adawa, ta bayyana kanta a matsayin mafi rinjaye a majalisa

PDP ta yi sharhi akan sauya shekar sanatocin APC 15 zuwa jam’iyyar adawa, ta bayyana kanta a matsayin mafi rinjaye a majalisa
Source: Depositphotos

A baya mun kawo labarin cewa, sanatocin jam’iyyar APC mai mulki guda goma sha biyar sun sanar da batun sauya shekarsu daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP sun amince da bukatar R-APC, sun shirya canza suna

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne ya karanta hakan a gaban zauren majalisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel