Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta dage zamanta har zuwa watan Satumba

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta dage zamanta har zuwa watan Satumba

A yau Talata, 24 ga watan Yuli, Majalisar dattawa ta dage zamanta na tsawon watanni biyu.

Dage zaman ya biyo bayan hare-hare da aka kaiwa shugaban majalisan dattawan a baya-bayan nan.

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 24 ga watan Yuli.

A safiyar yau ne dai jami’an tsaro suka kai mamaya ga Saraki da mataimakinsa, Ike Ekweremadu.

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta dage zamanta har zuwa watan Satumba

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta dage zamanta har zuwa watan Satumba
Source: Depositphotos

Yan majalisan za su dawo ne a ranar 25 ga watan Satumba.

A halin da ake ciki, mun samu labarin cewa sanatocin jam’iyyar APC mai mulki guda goma sha biyar sun sanar da batun sauya shekarsu daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.

KU KARANTA KUMA: Bamu da masaniya akan mamaya da aka kai gidan Saraki – Yan sanda

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne ya karanta hakan a gaban zauren majalisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel