Zargin karkatar da kudade: EFCC ta gayyaci mataimakin shugaban majalisa Ekweremadu

Zargin karkatar da kudade: EFCC ta gayyaci mataimakin shugaban majalisa Ekweremadu

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta gayyaci mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya bayyana a ofishinta don amsa tambayoyi game da zarginsa da karkatar da kudaden gwamnati.

A wasikar gayyatar da aka aika a ranar 24 ga watan Yuli mai dauke da sa hannun direktan ayyuka na hukumar, Mohammed Abba, EFCC ta bukaci Ekweremadu ya bayyana a ofishin hukumar a yau Talata saboda ya amsa wasu tambayoyi.

A wasikar, hukumar EFCC tace tana bincike ne game da "zargin hadin baki da karkatar da kudaden gwamnati da kuma amfani da karfin ofishi wajen saboda dokokin aiki."

EFCC ta gayyaci mataimakin shugaban majalisa, Ekweremadu bisa zarginsa da karkatar da kudade

EFCC ta gayyaci mataimakin shugaban majalisa, Ekweremadu bisa zarginsa da karkatar da kudade

Hukumar ta bukaci Ekweremadu ya bayyana a ofishinta dake lamba 5 Fomela Street, Off Adetokumbo Ademola Crescent, Wuse II Abuja a ranar 24 ga watan Yulin shekarar 2018 da karfe 10 na safiya.

Hukumar tace wannan gayyatar ya yi dai-dai da sashi na 38(1) na dokar hukumar EFCC ta 2004.

Sai dai duk da wasikar gayyatar da aka aike masa, wasu tawagar jami'an yan sanda sun mamaye gidansa dake Apo Legislative Quaters dake Abuja a safiyar yau asabar duk da cewa yau ne ya kamata ya gabata a ofishin hukumar.

Har yanzu ba'a bayyana takamamen dalilin da yasa ake yiwa gidan Ekweremadu kawanya ba.

Kazalika, wasu yan sandan kuma sun mamaye gidan shugaban majalisa, Bukola Saraki, sai dai daga baya ya sulale cikin wata tsohuwar mota ya tafi majalisar dattawar inda ya jagoranci zaman majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel