Yanzu Yanzu: Murna ya kaure a majalisar wakilai yayinda sanatoci suka sauya sheka

Yanzu Yanzu: Murna ya kaure a majalisar wakilai yayinda sanatoci suka sauya sheka

Mambobin majalisar wakilai daga jam’iyyar PDP sun kasance cikin murna a yanzu haka kan sauya shekar da sanatocin jam’iyyar APCsuka yi a safiyar yau.

Mambobin, karkashin jagorancin mataimakin shugaban yan tsiraru, Mista Chukwuka Onyema, suna rera wakar adawa da APC a harabar majalisar dokoki.

Majalisar bata fara tattaunawarta na yau ba.

Yanzu Yanzu: Murna ya kaure a majalisar wakilai yayinda sanatoci suka sauya sheka

Yanzu Yanzu: Murna ya kaure a majalisar wakilai yayinda sanatoci suka sauya sheka

Yanzun nan Kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya iso majalisar inda ake ta ihun “Dogara”; “Dogara”; “Dogara.

KU KARANTA KUMA: Bamu da masaniya akan mamaya da aka kai gidan Saraki – Yan sanda

Mambobin majalisa yan PDP na sanya ran za’a samu masu sauya sheka a majalisar wakilai ma, tare da jin dadin cewa jam’iyyar ta fara komawa matsayinta na masu rinjaye.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel