Yanzu Yanzu: Jami’an tsaro sanye da kayan gida sun kai mamaya gidan Sanata Shehu Sanin a Abuja

Yanzu Yanzu: Jami’an tsaro sanye da kayan gida sun kai mamaya gidan Sanata Shehu Sanin a Abuja

Sanata Shehu Sani yace a sanar da shi cewa jami’an tsaro sanye da kayan gida sun je gidansa dake Abuja inda suka bukaci ganinsa bayan ya tafi Ofis.

Sani a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na twitter ya bayyana cewa an kaiwa gidansa mamaya. Sanatan ya kuma bayyana cewa a lokacin da suka isa gidan nasa sun nace kan cewa lallai yana nan.

Yanzu Yanzu: Jami’an tsaro sanye da kayan gida sun kai mamaya gidan Sanata Shehu Sanin a Abuja

Yanzu Yanzu: Jami’an tsaro sanye da kayan gida sun kai mamaya gidan Sanata Shehu Sanin a Abuja

Dan majalisan ya kara da cewa shi ya kasance mai neman sauyi domin ya taba fuskantar irin haka a baya.

KU KARANTA KUMA: Bamu da masaniya akan mamaya da aka kai gidan Saraki – Yan sanda

A halin da ake cikin, Legit.ng ta rahoto cewa sanatocin jam’iyyar APC mai mulki guda goma sha biyar sun sanar da batun sauya shekarsu daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne ya karanta hakan a gaban zauren majalisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel