Bidiyon yadda ‘Yan sanda su ka mamaye gidan Bukola Saraki kafin ya sulale

Bidiyon yadda ‘Yan sanda su ka mamaye gidan Bukola Saraki kafin ya sulale

- Dambar siyasa na cigaba da daukar zafi gabannin zaben 2019

- Da safiyar yau ne jami'an tsaro suka mamaye gidan shugaban majalisar dattijai

- Amma sai dai duk da haka ya samu ya sulale har ya halarci zaman majalisar na yau inda suka sanar da ficewarsu tare da wasu sanatoci 15

Da sanyin safiyar yau ne, jami'an farin kaya tare da hadin guiwar jami'an hukumar yaki da cin-hanci da rashawa wato EFCC suka yiwa gidan shugaban majalisar datijjai Abubakar Bukola Saraki kawanya da nufin hana shi fita daga gidansa dake Maitama a Abuja.

Kalli bidiyon yadda ‘yan sanda suka tsarewa Bukola Saraki da mataimakinsa

'Yan sanda sun tsare gidan Bukola Saraki da mataimakinsa

A cikin wani sakon kar ta kwana ta hanyar sada zumunta ta WhatApp da mai bashi shawara akan harkokin kasashen waje Bamikole Omisore, ya aikewa da jaridar Eagle Online. Omisore ya bayyana cewa shugaban majalisar ya fita daga gidansa ne da nufin amsa gayyatar da hukumar ‘yan sanda tayi masa, amma abin mamaki sai ga jami'an na yan sandan sun tare masa hanya.

Latsa nan don kallon bidiyon

A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban hukumar ‘yan sanda ta kasa, an bukaci shugaban majalisar ya bayyana a ofishin ‘yan sanda domin cigaba da masa tambayoyi game da fashi da makamin da aka yi a garin Offa.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Sanatoci 15 sun sauya sheka daga APC

Sai dai Saraki yace wannan ba komai bane face hana yunkurin ficewar wasu Sanatoci daga jam'iyyar APC, ya ce an tsara yau Talata da kuma Laraba a matsayin ranakun da za a fice daga jam'iyyar.

A wani rahoto mai kama da haka, an bayyana cewa an hango jami'an farin kaya dana hukumar yaki da cin-hanci da kuma yan sanda a kofar gidan mataimakin shugaban majalisar datijjai Dakta Ike Ekweremadu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel