Yanzu Yanzu: Sanatoci 15 sun sauya sheka daga APC

Yanzu Yanzu: Sanatoci 15 sun sauya sheka daga APC

Labari dake iso mana a yanzu sun nuna cewa sanatocin jam’iyyar APC mai mulki guda goma sha biyar sun sanar da batun sauya shekarsu daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne ya karanta hakan a gaban zauren majalisa.

Sanatocin da suka sauya sheka sune: Sanata Shaaba, Sanata Melaye, Sanata Shittu, Sanata Rafiu, Sanata Shehu Sani, Sanata Shitu Ubali, Sanata Isa Misau.

Yanzu Yanzu: Sanatoci 15 sun sauya sheka daga APC

Yanzu Yanzu: Sanatoci 15 sun sauya sheka daga APC

Sauran sun hada da: Sanata Hunkuyi, Sanata Gemade, Sanata Danbaba, Sanata Nafada, Sanata Monsurat, Sanata Tejuoso, Sanata Nazif, Sanata Kwankwaso.

KU KARANTA KUMA: Bamu da masaniya akan mamaya da aka kai gidan Saraki – Yan sanda

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a yayinda 'yan sanda suka tare kofar gidan shugaban majalisa Bukola Saraki don hana shi zuwa zaman majalisa, Sarkin ya yi dabara inda ya sulale cikin wata tsohuwar motar da ya tuka da kansa ya tafi majalisan ya bar yan sandan dake kofar gidansa suna gadi kamar yadda Sahara reporters ta wallafa.

'Yan sandan sunyi kawanya a gidan Saraki ne saboda rashin amsa gayyatar da hukumar tayi masa don ya amsa tambayoyi game da zargi da ake masa da hannu cikin fashin da akayi a wasu bankuna a Offa a kwanakin baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel