Gwamnatin Buhari na daf da kwace wasu miliyoyin kudade a hannun tsoffin ma'aikatan INEC

Gwamnatin Buhari na daf da kwace wasu miliyoyin kudade a hannun tsoffin ma'aikatan INEC

- Wasu manyan ma'aikata a INEC sun gurfana gaban alkali kan zarginsu da ake da rabauta da kudaden da aka raba don murde zaben 2015

- Yanzu haka mai shari'a ya basu kwanaki 12 don su bayyana yadda akai suka samu makudan kudaden ko a kwace su kwata-kwata

- EFCC ce dai tun farko ta maka jami'an a kotun sakamakon zarginsu da take

Rahotan da jaridar New Telegraph ta rawaito ya nuna cewa alkalin wata babbar kotu da ke zamanta Legas Muslim Sule Hassan, ya ba da umarnin cigaba da bincike tare da sanya takunkumi ga kudaden wasu tsofaffin ma'aikan hukumar zabe ta kasa INEC.

Hakan ya biyo bayan zargin samum kudade har miliyan 387 a cikin asusun bankunansu wanda hakan yasa ake tunanin yana da nasaba da zaben shekara ta 2015.

Kotu ta bayar da umarnin kwace miliyoyin kudaden da aka boye a bankuna mallakar tsoffin ma’aikatan INEC

Kotu ta bayar da umarnin kwace miliyoyin kudaden da aka boye a bankuna mallakar tsoffin ma’aikatan INEC

Hakan ya biyo bayan karar da hukumar yaki da cin-hanci da rashawa tayi ta hannun jami'inta karkashin sashi na 17 na dokar karbar cin hanci na shekara ta 2014.

Bayanan da Legit.ng ta tattara ya nuna cewa masu laifin da suka hada da Gabriel Oke, Victor Chukwuani, Okesiji Adeniran da Torgba Nyitse, dukkansu sun bayyana gaban kotun domin sauraren laifi guda da ake tuhumarsu.

KU KARANTA: Zargin karkatar da kudade: EFCC ta gayyaci mataimakin shugaban majalisa Ekweremadu

Alkalin ya bawa kowannen su tsawon sati biyi domin sake bayyana gaban kotu domin yin cikakkaen bayanin da kotun zata amince da shi cewa kudaden basu da alaka da zaben shekara ta 2015, in kuma ba haka ba kotu zata damka kudaden ga gwamnati.

Kotun ta dage zaman har sai 6 ga watan Agustan shekarar nan.

A cikin wata takardar korafi da jami'in hukumar ta EFCC ya aike ga kotun ya ce tsoffin ma'aikatan hukumar zaben ta kasa sun amfana daga cikin bilyan 23 da tsohon ministan gwamnatin baya ya bayar domin shirya magudi a yayin zaben.

Ya kara da cewa sun mallaki wannan makudan kudade ne ta hanyar wata kungiya mai zamanta kanta wanda bincike ya nuna, kuma tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Maurice Iwu shi ne shugaban kungiya.

Sannan ya ce ya zuwa yanzu hukumar ta EFCC ta samu miliyan 387 daga cikin miliyan 510 da ake zargin tsofaffin ma'aikan hukumar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel