Fashin Offa: Hukumar 'Yan Sanda sun nemi Saraki sama da kasa sun rasa

Fashin Offa: Hukumar 'Yan Sanda sun nemi Saraki sama da kasa sun rasa

Ana zargin cewa shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya tsere biyo bayan gayyatar da hukumar 'yan sandan Najeriya tayi masa, domin ya amsa wasu tambayoyi da suke da alaka da fashin da aka yi a garin Offa na jihar Kwara a watan Afrilun da ya gabata

Fashin Offa: Hukumar 'Yan Sanda sun nemi Saraki sama da kasa sun rasa

Fashin Offa: Hukumar 'Yan Sanda sun nemi Saraki sama da kasa sun rasa

Ana zargin cewa shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya tsere biyo bayan gayyatar da hukumar 'yan sandan Najeriya tayi masa, domin ya amsa wasu tambayoyi da suke da alaka da fashin da aka yi a garin Offa na jihar Kwara a watan Afrilun da ya gabata.

A jiya ne hukumar 'yan sandan kasar nan ta bukaci Saraki da ya bayyana a gaban ta yau dinnan a Abuja domin amsa tambayoyi.

DUBA WANNAN: An kama wanda ya kashe Diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo

Bayan haka a wata sanarwa data fito daga bakin mai bawa Saraki shawara na musamman Yusuph Olaniyonu, ya zargi jam'iyyar APC da hannu a neman da hukumar 'yan sandan ke yiwa Sarakin.

A lokacin da wakilin mu ya isa gidan Saraki da misalin karfe 8 na safiyar yau a Maitama District, ya ga motoci a ajiye a gidan da kuma ma'aikata suna gabatar da ayyukan su na yau da kullum.

Daga baya dai mun samu labarin cewar Saraki ya gudu, bayan da wakilan mu suka kira Olaniyonu don ya bayyana inda Maigidan nashi yake, sai yace shima bai da masaniya.

Ya ce ya zo gidan da safe, sai yaga jami'an 'yan sanda a kofar gidan, dalilin da ya saka shi juyawa kenan.

Bayan haka kuma mai magana da yawun mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, Uche Anichukwu, ya bayyanawa manema labarai a wayar salula cewar 'yan sanda sun yiwa gidan mai gidan nasa tsinke shima.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel