Toh fah! An gano Bukola Saraki ya shiga majalisa ya bayan gida

Toh fah! An gano Bukola Saraki ya shiga majalisa ya bayan gida

A yayinda 'yan sanda suka tare kofar gidan shugaban majalisa Bukola Saraki don hana shi zuwa zaman majalisa, Sarkin ya yi dabara inda ya sulale cikin wata tsohuwar motar da ya tuka da kansa ya tafi majalisan ya bar yan sandan dake kofar gidansa suna gadi kamar yadda Sahara reporters ta wallafa.

'Yan sandan sunyi kawanya a gidan Saraki ne saboda rashin amsa gayyatar da hukumar tayi masa don ya amsa tambayoyi game da zargi da ake masa da hannu cikin fashin da akayi a wasu bankuna a Offa a kwanakin baya.

Yanzu Yanzu: Saraki ya sulale cikin majalisa a wata tsohuwar mota

Yanzu Yanzu: Saraki ya sulale cikin majalisa a wata tsohuwar mota

KU KARANTA: R-APC zata iya tsayar da dan takarar shugaban kasa - Buba Galadima

Sai dai wasu Sanatocin masu goyon bayan Bukola Saraki sunyi ikirarin cewa 'yan sandan na son tsare Saraki a caji ofis ne yayin da Sanatocin kungiyar PSG su kuma zasu tsige shi a majalisa.

Wata majiyar ta kuma ce Sanata Bukola Saraki yana gab da ficewa daga jam'iyyar ta APC a yau sannan ya dage zaman majalisar har illa masha Allah.

A halin yanzu dai ba'a sani ko Bukola Saraki zai amsa gayyatar hukumar 'yan sandan ba duk da cewa a yammacin jiya Litinin yace zai tafi ya amsa dukkan tamboyin da suke son yi masa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel