Yanzu Yanzu: Kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP sun amince da bukatar R-APC, sun shirya canza suna

Yanzu Yanzu: Kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP sun amince da bukatar R-APC, sun shirya canza suna

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jiya ta amince da bukatar kungiyar sabuwar APC a jam’iyar gabannin zaben 2019.

An yanke shawarar ne a taron kwamitin masu ruwa da tsaki na 80 wanda jam’iyyar ta gudanar a ranar Litinin.

Wani hukunci da kwamitin NEC ta sake dauka shine dakatar da manyan mambobin jam’iyyar na babin jihar Ogun ciki harda dan majalisa mai wakiltn Ogun ta yamma, Buruji Kashamu. Sauran mutanen da aka dakatar sune Semiu Sodipo, Segun Seriki da kuma Dayo Adebayo.

Yanzu Yanzu: Kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP sun amince da bukatar R-APC, sun shirya canza suna

Yanzu Yanzu: Kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP sun amince da bukatar R-APC, sun shirya canza suna
Source: Depositphotos

Da yake jawabi ga manema labarai a karshen taron, kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya kuma bayyana cewa kwamitin NEC ta kafa wata kwamiti kan batun canza suna.

KU KARANTA KUMA: Bamu da masaniya akan mamaya da aka kai gidan Saraki – Yan sanda

Ya kara da cewa yunkurin shiga kotu kan zaben gwamnan jihar Ekiti ya samu yardan shugabannin jam’iyyar a fadin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel