Ya kamata Buhari yayi murabus daga mukaminsa – In ji wani babban malamin addini

Ya kamata Buhari yayi murabus daga mukaminsa – In ji wani babban malamin addini

- Shugaba Muhammadu Buhari na cigaba da fuskantar adawa daga malaman addini

- Bayan sukarsa da Sheikh Abubakar Gumi ke yawaita yi, yau ma wani malamin addinin Kirista ya yi kira da ya sauka daga mukaminsa

Wani babban malamin addini daga Cocin Living Faith Bishop David Oyedepo ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya sauka daga mukaminsa na shugaban kasa, sakamakon kashe-kashen da ake fama da su a tsakanin Fulani da Manoma a fadin kasar nan.

Ya kamata Buhari yayi murabus daga mukaminsa – In ji wani babban malamin addini

Ya kamata Buhari yayi murabus daga mukaminsa – In ji wani babban malamin addini

Malamin ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadin da ta gabata ta hanyar kafar sadarwa ta YouTube, wanda aka dora a shafin sada zumunta na Cocin.

Wannan yana zuwa ne a lokacin da wasu fitattun masu wa'azin Kirista suka dinga kira akan shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus, wadanda suka hadar da Archbishop na Cocin Roman Katolika da ke Abuja wato John Kadinal Onaiyekan da kuma tsohon Archbishop na Cocin Katolika dake Legas Kadinal Anthony Olubunmi Okogie, bisa dalilin rashin samar da tsaron da zai kare rayukan al'ummar kasar nan.

KU KARANTA: Da duminsa: Buba Galadima, Shugaban R-APC ya yi hatsari

Oyedepo ya bayyanawa dandazon magoya bayansa cewa shi ba dan wata jam’iyya ba ne, amma ba zai kasance a raye ba, sannan ya zuba idanu ana ta kashe-kashe ba tare da ya tofa albarkacin bakin sa ba, musamman kan rikicin da ake fama da shi a yankin Arewa ta tsakiya, wanda ake zargin fulani makiyaya da aikatawa.

Malamin ya gargadi ‘yan kasar nan akan kudurin da gwamnatin tarayya ta dauka na samarwa da Fulani guraben kiwo a fadin kasar nan.

Inda ya ce, "Najeriya ba kasar Fulani ba ce su kadai, domin babu wata yarjejeniyar da ta nuna haka, saboda haka babu wani dalili da zai sanya a dinga baiwa wadansu mutane gurin zama ko gurin kiwo a yankunan da ba nasu ba".

A karshe ya ce dole a tashi tsaye domin magance wannan masifar kashe-kashen da ake zargin Fulani da aikatawa, tare kuma da jaddada kiransa ga shugaba Muhammadu Buhari da yayi gaggawar sauka daga mukaminsa na shugaban kasa.

"Abinda ya fi dacewa da shugaba Buhari shi ne tun da baya tabuka komai kawai ya sauka daga kan mukaminsa, wannan shi ya dacewa da shi, har a yankin arewacin kasar nan wasu malaman addinin musulunci suna kira akan shugaba Muhammadu Buharin ya sauka daga kan mulkinsa" in ji Bishop Oyedepo

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel