Bamu da masaniya akan mamaya da aka kai gidan Saraki – Yan sanda

Bamu da masaniya akan mamaya da aka kai gidan Saraki – Yan sanda

Rundunar yan sandan Najeriya a ranar Talata tace bata da masaniya akan mamaya da jami’an tsaro suka kai gidan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Kakakin rundunar, DCP Jimoh Moshood yace ba shi da masaniya akan lamarin.

“Bani da masaniya akan haka. Kune kuka sanar mani yanzu,” ya fadama majiyarmu akan wayar tarho.

Moshood yace shi dai yana masaniya akan wasika da aka bukaci Saraki ya gabatar da kansa domin amsa tambayoyi yau da misalin karfe 8am.

Bamu da masaniya akan mamaya da aka kai gidan Saraki – Yan sanda

Bamu da masaniya akan mamaya da aka kai gidan Saraki – Yan sanda

A safiyar ranar Talata ne yan sanda suka tsaida ayarin motocin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a Lake Chad Junction, Maitama Abuja.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta rufe sakamako mamaya da aka kai gidajen Saraki da Ekweremadu

A ranar Litinin, rundunar yan sandan sun aika da wasikar gayyata zuwa ga Saraki inda suka bukaci ya gurfana a gaban masu bincike a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel