Majalisar dattawa ta rufe sakamako mamaya da aka kai gidajen Saraki da Ekweremadu

Majalisar dattawa ta rufe sakamako mamaya da aka kai gidajen Saraki da Ekweremadu

Ana sa ran cewa majalisar dattawa bazata yi zama a ranar Talata, 24 ga watan Yuli ba, sakamakon mamaya da aka kai gidajen manyan shugabanninta, Bukola Saraki da Ike Ekweremadu.

Jami’an tsaro daga rundunar yan sandan Najeriya, hukumar yan sandan DSS, da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sun kewaye gidajen shugabannin biyu, a safiyar ranar Talata, jaridar Punch ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa da ake martani akan wannan ci gaba, wani hadimin Ekweremadu, wadda ya ki yarda a sanyo sunansa, ya bayyana cewa majalisar masu rinjaye ba za su yi zama ba, kamar yadda ya kamata a fara zama da karfe 9am.

Majalisar dattawa ta rufe sakamako mamaya da aka kai gidajen Saraki da Ekweremadu

Majalisar dattawa ta rufe sakamako mamaya da aka kai gidajen Saraki da Ekweremadu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jami'an hukumar SARS na ofishin yan sandan Abuja sun tare shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, da safen nan sun hanashi fita daga gidansa da ke unguwar Maitama dake Abuja.

KU KARANTA KUMA: Ba da kudi ka shiga wasa: An gano barnar da ake yi a wasan kwallon kasar nan

Jami'an yan sandan sun dira gidansa ne misalin karfe 6 na safe kuma sun hana kowa fitowa daga gidan.

Kana sun hana mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, fitowa yayinda suka tsare gidansa dake Apo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel