Ko kun san yawan kwararrun likitoci 'yan Najeriya dake aiki a kasar Afrika ta Kudu

Ko kun san yawan kwararrun likitoci 'yan Najeriya dake aiki a kasar Afrika ta Kudu

Rahotanni sun nuna cewa akwai kwararrun likitoci sama da 5,000 wadanda suke aiki a asibitoci daban - daban a kasar Afrika ta Kudu

Kalli yawan kwararrun likitoci 'yan Najeriya da kasar Afrika ta Kudu kwashe daga Najeriya
Kalli yawan kwararrun likitoci 'yan Najeriya da kasar Afrika ta Kudu kwashe daga Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa akwai kwararrun likitoci sama da 5,000 wadanda suke aiki a asibitoci daban - daban a kasar Afrika ta Kudu.

Sanarwar ta fito daga bakin mataimakin jakadan Najeriya na kasar Afrika ta Kudun, Mr David Abraham, shine ya bayyanawa manema labarai jiya a babban birnin tarayya Abuja.

DUBA WANNAN: An kama wanda ya kashe Diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo

Abraham ya ambaci babban jakadan Najeriyan na kasar, Godwin Adama, yayi bayanin a lokacin da kungiyar likitoci ta kasar Afrika ta kudun suka kaiwa babban jakadan Najeriyan ziyara a ofis nashi dake babban birnin Johannesburg, wanda Sakataren kungiyar, Dr Emeka Ugwu, ya jagoranta.

“Hakan yana nuna cewa kowanne asibiti a kasar Afrika ta Kudu yana da kwararrun likitoci ‘yan Najeriya.

Ya ce kasar Afrika ta Kudu ta cika da kwararrun ma’aikata ‘yan Najeriya wadanda suke bada babbar gudummawa wurin cigaban kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel