Jam'iyyar PDP ta dakatar da wasu jiga - jigan ta guda 4

Jam'iyyar PDP ta dakatar da wasu jiga - jigan ta guda 4

Kwamitin babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta bada sanarwar dakatar da Sanata Buruji Kashamu da wasu jiga - jigan jam’iyyar guda uku daga jam’iyyar, saboda kama su da jam’iyyar tayi da hannu wurin yiwa jam’iyyar magudi

Jam'iyyar PDP ta dakatar da wasu jiga - jigan ta guda 4

Jam'iyyar PDP ta dakatar da wasu jiga - jigan ta guda 4

Kwamitin babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta bada sanarwar dakatar da Sanata Buruji Kashamu da wasu jiga - jigan jam’iyyar guda uku daga jam’iyyar, saboda kama su da jam’iyyar tayi da hannu wurin yiwa jam’iyyar magudi.

Sauran mutane uku wadanda aka dakatar tare da Buruji, sun hada da Semiu Sodipo, Bayo Adebayo da kuma Segun Seriki.

DUBA WANNAN: An kama wanda ya kashe Diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo

Jam’iyyar na zargin su da hada baki da jam’iyyar APC ta jihar Ekiti wurin yi musu magudi a zaben gwamnan da ya gabata a jihar.

“Jam’iyyar ta dauki wannan matakin ne, domin ya zama darasi ga wasu ‘yan jam’iyyar masu irin wannan halayen, inji Sakataren jam’iyyar, Mr Kola Ologbondiyan.

Taron da kwamitin ta gabatar wanda Shugaban jam’iyyar, Prince Uche Secondus ya jagoranta, taron ya samu halartar gwamnoni da wasu jiga - jigai na jam’iyyar daga fadin kasar nan.

A karshe jam’iyyar ta yanke hukuncin canja sunanta daga PDP zuwa wani suna daban kafin zuwan lokacin babban zabe na shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel