Rokon R-APC da muke yi ba yana nufin tsoro bane - Oshiomhole

Rokon R-APC da muke yi ba yana nufin tsoro bane - Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole, ya bayyana dalilin da yasa yake ta rokon mambobin kungiyar sabuwar APC da kada su bar APC. Yace hakan da yake yi ba yana nufin tsoro bane.

Oshiomhole ainda ake Magana a wajen kaddamar da wata takarda daga Sanata Bukar Abba Ibrahim (APC, Yobe na yamma), ya bayyana cewa rokon da ake yiwa fusatattun mambobin duk kokari ne na wanzar da zaman lafiya da yin adalci ga wadanda suka cancanta.

Ya bayyana cewa hakan ba wai sakamakon tsoro bane.

Rokon R-APC da muke yi ba yana nufin tsoro bane - Oshiomhole

Rokon R-APC da muke yi ba yana nufin tsoro bane - Oshiomhole

Oshiomhole yace: “Daga karshen mako har zuwa ranar Litinin, ana ta kawo labarai daban-daban na cewa bana bacci tsakanin makon da ya gabata sakamakon ganawar tsakar dare da fusatattun mambobin jam’iyyar, wadda suka ce ina ta roko kan kada su fice daga jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Ba da kudi ka shiga wasa: An gano barnar da ake yi a wasan kwallon kasar nan

“A wasu daga cikin rahotannin, jita-jitan ya kai har na cewa na bayar da toshiyar baki ga masu fafutukar a kokarinsu na hana su ficewa daga jam’iyyar. Ba zan ce komai kan haka ba sai dai abun d azan ce shine, ina ta ganawa da masu fafutuka na jam’iyar kan rashin adalcin da suke ganin jam’iyar tayiwa wasu jiga-jigan su. Bana hana kaina bacci kamar yadda ake fadi, sannan kuma babu wani toshiyar baki da na bayar.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel