Osun 2018: ‘Yan PDP ba su yarda da sakamakon zaben fitar da gwanin da aka yi ba

Osun 2018: ‘Yan PDP ba su yarda da sakamakon zaben fitar da gwanin da aka yi ba

Wasu daga cikin manyan Jam’iyyar PDP a Kasar Yarbawa ba su ji dadin sakamakon zaben fitar da gwani na Jam’iyyar adawan da aka yi Jihar Osun ba. 'Dan Majalisar Jihar Ademola Adeleke ne yayi nasara a zaben da aka yi a makon da ya wuce.

Osun 2018: ‘Yan PDP ba su yarda da sakamakon zaben fitar da gwanin da aka yi ba

'Yan PDP sun nuna cewa ba su yarda da Ademola Adeleke ba

Manyan Jam’iyyar PDP sun yi zanga-zanga inda su ka nuna cewa ba su amince da sakamakon zaben da aka yi ba. ‘Yan Jam’iyyar sun nuna cewa su na bayan Akin Ogunbiyi ne wanda ya zo na biyu a zaben bayan Sanata Ademole Adeleke.

KU KARANTA: An shirya mana makarkashiya da ‘Yan Sanda domin a hana mu ficewa daga APC – Saraki

Wadanda su kayi zaben sun nuna cewa an yi rashin gaskiya a wajen zaben na tsaida ‘Dan takara. Funso Babarinde wanda yana cikin manyan PDP a Jihar yayi magana bayan zaben inda yace an yi cuwa-cuwa domin ganin Adeleke yayi murna.

Wadanda sakamakon zaben ya fusata sun ce Dr. Akin Ogunbiyi ne yayi nasara amma aka murde. Shi ma dai Ogunbiyi wanda ya sha kashi yace ba zai yarda da sakamakon zaben ba domin kuwa da karfi da yaji aka tika shi da kasa.

Dama kun ji labari cewa Sanatan da ya saba tika rawa a Majalisa Ademola Adeleke ya samu tutar takarar Gwamnan inda ya doke Akin Ogunbiyi da kuri’a 7. Adeleke zai gwabza ne da ‘Dan uwan Tinubu a takarar Gwamnan Osun din.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel