Saraki ya bayyana munakisar da ake yi da ‘Yan Sanda na hana wasu manyan ‘Yan Majalisa barin APC

Saraki ya bayyana munakisar da ake yi da ‘Yan Sanda na hana wasu manyan ‘Yan Majalisa barin APC

- Saraki ya maida kakkausan martani bayan ‘Yan Sanda sun gayyace sa gaban su

- Shugaban Majalisar yace ana neman garkame sa yau domin hana su barin APC

A yau ne ake sa rai cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki zai hallara gaban ‘Yan Sandan Najeriya inda ake zargin sa da hannu cikin laifin wani fashi da makami da aka yi a Garin Offa, Saraki yace yana sa rai gaskiya tayi halin ta.

Shugaban Majalisa Bukola Saraki yace ‘Yan Sanda na shirya masa sharri

Shugaban Majalisa Bukola Saraki yace ‘Yan Sanda na shirya masa sharri

Shugaban Majalisar ya maida martani game da sammacin da aka yi masa inda ya nuna cewa akwai lauje cikin nadi a lamarin. Bukola Saraki ta bakin wani hadimin sa yake cewa an shirya wannan sammaci ne domin hana sa barin APC.

Yusuf Olaniyonu ya fitar da wannan jawabi jiya da dare inda yace tuni Jami’an ‘Yan Sandan su ka gama binciken su amma su ka sake aika masa gayyata domin a hana wasu ‘Yan Majalisar Kasar ficewa daga Jam’iyyar APC mai mulki a makon nan.

KU KARANTA: Shugaban Majalisa Bukola Saraki ya fara shawarar abin yi a a 2019

‘Yan Sandan sun shirya rufe Bukola Saraki ne yau zuwa gobe domin gudun abin da ake ji na cewa su na shirin barin APC. Shugaban Majalisar dai ya bayyana cewa maganar tserewan sa daga Jam'iyyar APC ba abu bane da zai dauki mataki shi kadai.

Shi dai Bukola Saraki ya rantse cewa ba shi da hannu a laifin da ake zargin shi da su kuma yace ‘Yan Sanda sun san da haka sai dai kurum a saka siyasa a lamarin. Saraki yace ana yi wa shi da Abokan tafiyar rashin adalci a tafiyar ta APC.

Dama can kun ji cewa Bukola Saraki ya fara shawarar abin yi a 2019. Sanata Bukola Saraki na tunanin inda zai sa gaba bayan ya gana da Shugaba Buhari kwanaki. Abokan siyasar sa dai na kira ya bar Jam’iyyar APC ya koma Jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel