Maganar ba ta wuce ba: Shugaban rundunar ‘yan sanda ya gayyaci Bukola a kan fashin Offa

Maganar ba ta wuce ba: Shugaban rundunar ‘yan sanda ya gayyaci Bukola a kan fashin Offa

Shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa (IGP), Ibrahim Idris, ya aikewa shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, takardar gayyatar ya bayyana a ofishin bincike na hukumar da safiyar yau.

Jaridar TheCable ta rawaito cewar, Idris ya aike da wasikar neman Saraki ya bayyana a ofishin na ‘yan sanda ne domin amsa tambayoyi a kan fashin garin Offa na jihar Kwara da aka yi tun watan Afrilu.

A takardar da hukumar ‘yan sanda, ta ofishin IG Idris, ta aikewa Saraki da yammacin jiya, Litinin, an bukaci ya bayyana da safiyar yau, Talata, da karfe 8:00 na safe domin cigaba da bincike a kansa.

Maganar ba ta wuce ba: Shugaban rundunar ‘yan sanda ya gayyaci Bukola a kan fashin Offa

Idris da Saraki

Tun da dadewa hukumar ‘yan sanda ta sanar da cewar ‘yan fashin Offa da ta kama sun shaida mata cewar suna yiwa Saraki aiki ne.

Tun a wancan lokacin, hukumar ‘yan sanda ta bukaci Saraki ya gabatar da kansa domin amsa tamboyi kafin daga bisani ta umarce shi ya aiko da jawabinsa a rubuce.

DUBA WANNAN: Batanci ga ma'aiki: Jami'an tsaro sun mamaye makaranta da dalibi ya zagi annabi

Saidai tun a wancan lokacin, gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya bayyana cewar kuskure ne a alakanta shi da Saraki da fashi da makami.

Kazalika Saraki da kansa ya yi watsi da batun zargin da ake yi masa na hannu a cikin fashin garin Offa. Saidai har yanzu bai musanta cewar ‘yan fashin yaransa dake masa bangar siyasa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel