An cafke wata budurwa bisa laifin sayarwa Daliban makaranta wiwi a Kano

An cafke wata budurwa bisa laifin sayarwa Daliban makaranta wiwi a Kano

- A yunkurin da gwamnati da jama'ar Kano suke na takawa harkar shaye-shaye birki, anyi ram da wata matashiyar mai siyarda wiwi ga dalibai

- Har an mika ta ga jami'ian tsaro don bincike

A kokarin da budurwa keyi na sayar da tabar wiwi ga dalibai, jami'an tsaro sun damke.

Budurwar dai an kama ta ne a lokacin da ta ke tsaka da sayarwa da daliban kwalejin gwamnatin tarayya da ke kano wato FCE jim kadan da fara cin kasuwarta ta ne aka damke, inda nan take ta amsa laifinta yayinda akai mata ca.

An cafke wata budurwa bisa laifin sayarwa da daliban makaranta wiwi a Kano

An cafke wata budurwa bisa laifin sayarwa da daliban makaranta wiwi a Kano

KU KARANTA: Wasu dalilai ne suka kai ni ga lalata karamar yarinya – Inji dan shekara 52

Rahotanni sun bayyana cewa lokacin da ake bincikarta sai ta kama zubar da hawaye tare da bayyana cewa hakika tana sayar da tabar wiwi din kuma tana da kwastomomi.

A karshe a damkata ga rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano domin zurfafa bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel