Jama’a sun fara kira a inganta tsaro bayan an kashe mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Jama’a sun fara kira a inganta tsaro bayan an kashe mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Jama’a sun hurowa Gwamnati wuta ayi maganin satar jama’a da ake yi

- Masu garkuwa da mutane sun saba tsare hanyar Kaduna zuwa Abuja

Mun samu labari cewa an fara hurowa Gwamnatin Tarayya wuta tayi maganin satar jama’ar da ake yi a Kasar nan. Jama’a sun fara kira ne Gwamnatin Najeriya ta kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Kaduna cikin kwanakin nan.

Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kaduna Dr. Aminu Shagali yayi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna ta inganta tsaro a Jihar. Hakan na zuwa ne bayan da aka kashe dinbin mutane kwanan nan a hanyar Garin Jere zuwa Birnin Tarayya Abuja.

KU KARANTA: An nada sabon Sardaunan Jihar Katsina bayan rasuwar Commassie

Dr. Aminu Shagali ta shafin Tuwita ya bayyana cewa Gwamnatin ta Jihar Kaduna na bakin kokari na ganin an daina barna a hanyar Kaduna zuwa Abuja. Kakakin Majalisar yace idan ba ayi maganin wannan matsala ba za ta ci kowa nan gaba.

Cikin ‘yan kwanakin nan ne aka kashe wata tsohuwar Kwamishinan Jihar Katsina Farfesa Halima Sadiya Idris a hanyar Abuja zuwa Kaduna. A ranar Lahadin ne dai kuma aka kashe mutane da dama har wasu manyan Jami’an tsaro na Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel