Zan bayyana jam’iyyar da nake a karshen mako - Ortom

Zan bayyana jam’iyyar da nake a karshen mako - Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa zai bayyana makomar siyasarsa kafin karshen wannan makon yayinda yayi kira ga yan takaran gwamna karkashin PDP a Benue da kada su bata gwanjinsu akan batun sauya shekarsa.

Ortom wanda ke maida martani gay an takarar gwamna a jihar da suka nuna rashin amincewa da dawowarsa jam’iyyar ya bayyana cewa yana daga cikin tubalin PDP a jihar sannan bai bukatar tuntubar kowani dan takarar gwamna idan yana son komawa jam’iyyar.

Da yake Magana a madadinsa, babban hadiminsa akan kafafen watsa labarai, Tahav Agerzua a bayyana cewa har yanzu bai fadama kowa cewa zai sauya sheka ba.

Zan bayyana jam’iyyar da nake a karshen mako - Ortom

Zan bayyana jam’iyyar da nake a karshen mako - Ortom

A cewar gwamnan, “Bana bukatar yardarsu kafin na koma jam’iyyar PDP, sannan ban sanar da kowa cewa zan koma PDP ba.”

KU KARANTA KUMA: Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Gwamnan ya bayyana cewa zai magance lamarin idan lokacin yin hakan yayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel