Da dumi-dumi: Gobara ta kama gidan gwamnatin jihar Osun

Da dumi-dumi: Gobara ta kama gidan gwamnatin jihar Osun

Labarin da ke shigowa yanzu na nuna cewa ofishin gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, da ke Abere jihar Osun ya kama da wuta kuma jami’an kawar da gobaran.

Game da cewar wani idon shaida, gobarar ta fara misalin karfe 4 na yamma ne kuma abin ya yi tsanani sanadiyar rashin budewan kofar shiga ofishin.

Kwamishanan yada labaran jihar, Adelani Baderinwa, a wata jawabi yace: "Hadarin wutan ya faru ne sanadiyar matsalar wutar lantarki yayinda na'urar sanyaya yanayin ofishin gwamnan ya samu matsala."

Baderinwa ya daurawa kamfanin wutan lantarkin garin laifin wannan hadari inda ya ce rashin bada isasshen wutan lantarki ne ya sabbaba haka.

Ya kara da cewa babu abinda ya kone a cikin ofishin.

Yace: (Kamfanin wutan) sun gaza bayar da wutan ke ake bukata,"

Yayi kira da kamfani IBEDC da su hana sake faruwan irin wannan hadari ta hanyar bin dokokin raba wuta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel