Yadda wata Ma’aikata tayi facaka da Biliyan 5.7 wajen kallace-kallacen DSTV

Yadda wata Ma’aikata tayi facaka da Biliyan 5.7 wajen kallace-kallacen DSTV

- An gano yadda wasu Hukumomin Gwamnati ke barna da kudi

- Hukumar NSITF ta kashe makudan kudi wajen wasu alawus

Wani bincike da Ma’aikatar kwadago na Kasar nan ta soma ya nuna yadda wata Ma’aikata tayi facaka da mahaukatan kudi wajen kallon talabijin a tsakanin 2013 zuwa 2017. Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari ne tayi wannan bincike kwanan nan.

Yadda wata Ma’aikata tayi facaka da Biliyan 5.7 wajen kallace-kallacen DSTV

An yi fatali da sama da Biliyan 5 wajen kallon talabijin a Ma’aikatar NSITF

Ministan Kwadago na Najeriya Chris Ngige ya sa ayi masa bincike kan zargin da ke yawo na cewa an yi faka da wasu kudi a Hukumar NSITF. Ana kishin-kishin din cewa Ma’aikatar ta kashe Biliyan 5.7 wajen ba Ma’aikata kudin kallon DSTV.

KU KARANTA: Wani matashi ya yi ma abokinsa duka daya har lahira akan N100

Ishaya Awotu wanda shi ne Shugaban kwamitin da aka nada yayi wannan bincike ya nuna yadda NSITF ta kashe wadannan makudan kudi wajen bada alawus na kallon tashoshi a talabijin. An ware wannan kudi ne ba tare da sa hannun Hukuma ba.

Bayan nan dai Hukumar NSITF ta kasar ta warewa Ma’aikatan ta alawus iri-iri wadanda su ka hada da na kudin mota da na tufafi. An yi wannan aiki ne duk ba tare da sa hannun Hukumar da ke kula da albashi da alawus din Ma’aikatan Najeriya ba.

Hukumar NSITF ta kashe makudan kudi wajen wasu alawus ne dai da ba gane kan su ba. Binciken da aka yi ya nuna cewa ana fitar da kudi domin zuwa Kasashen waje yin kwas ba bisa ka'ida ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel